Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Girke Jami’an Tsaro a Hukumar Inshorar Lafiya Ta Najeriya


Wasu daga cikin 'yan sandan Najeriya a lokacin da suke bakin aiki
Wasu daga cikin 'yan sandan Najeriya a lokacin da suke bakin aiki

Yayin da babban Sakataren hukumar inshorar lafiya ta Najeriya ya koma bakin, ana ci gaba da samun ra’ayi mabanbanta kan komawarsa aiki, bayan dakatar da shi da aka yi na tsawon watanni takwas, lamarin da ya janyo cece-ku-ce.

An girke jami’an ‘yan sanda a kofar hukumar inshorar lafiya ta Najeriya da ke Abuja, yayin da babban sakatarenta, Furfesa Usman Yusuf ya koma bakin aiki.

A watan Yunin da ya gabata, Ministan kiwon lafiyan kasar, Isaac Adewole, ya dakatar da Furfesa Yusuf, bisa zargin almubazzaranci da kudaden hukumar.

Daya daga cikin wakilan Muryar Amurka a Abuja, Hassan Maina Kaina, ya ruwaito cewa ya ga an girke motocin ‘yan sanda a kofar hukumar.

A makon da ya gabata, shugaban Najeriya ya mayar da Yusuf bakin aiki, inda ya nemi ya hada kai da ministan kiwon lafiya Adewole su yi aiki tare.

Wannan maido da Furfesa Yusuf da aka yi, ya janyo cece-ku-ce tare da dasa alamar tambaya kan akidar gwamnatin Buhari ta yaki da cin hanci da rashawa.

Bayanai da wakilinmu ya tattara a ma’aikatar, sun nuna cewa a tsakanin ma’aikatar ma, akwai rarrabuwar kawuna kan dawo da Furfesa Yusuf, yayin da wasu ke maraba, wasu kuwa adawa suke yi da matakin.

Saurari rahoton Hassan Maina Kaina domin jin abin da bangarorin biyu ke cewa:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:44 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG