Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Sama Na Britaniya Sun Kashe Mayakan ISIS a Syria


Firayim Ministan Birtaniya David Cameron
Firayim Ministan Birtaniya David Cameron

Firayim Ministan Birtaniya David Cameron ya sanar cewa sojojin saman kasarsa sun kashe mayakan ISIS uku da wasu 'yan asalin kasarsa biyu watan jiya.

Yau kasar Birtaniya ta sanarda kashe wasu mayakan ISIS a Syria da suka hada da 'yan asalain kasar biyu.

Mr David Cameron yace harin da sojojin Birtaniya suka kai ranar 21 ga watan Augusta ta yin anfani da jiragen sama masu sarafa kansu tamkar na kare kai ne saboda akwai kwararan shaidu cewa mayakan suna shirin kai hari cikin Birtaniya.

A cikin jawabin da yai yiwa majalisar dokokin Britaniya Mr. Cameron yace Rayaad Khan da wasu biyu da suka hada da dan Birtaniya an kashesu ne yayin da suke tafiya cikin wata mota kusa da birnin Raqqa dake zama fadar ISIS a Syria.

Yayinda kasar Birtaniya ta kasance cikin kawanncen dake kai hari kan ISIS cikin kasar Iraqi kuma tana anfani da jiragen sama masu sarafa kansu wajen tara bayanan siri, mayakan samanta basu taba auna hari kan ISIS din ba sai wannan karon a watan Augusta.

Kawo yanzu an kiyasta 'yan asalin Birtaniya 500 zuwa 600 ne suke zuwa Syria da suka hadu da dubban mayakan sa kai daga kasashen duniya da suka zo shiga ayarin kungiyar ISIS wadda ta hada wani bangaren Iraqi da na Syria a matsayin kasa daya da ta kira daular Islama.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG