Kasar Faransa za ta fara sintirin jiragen sama a sararin saman kasar Syria, gabanin yiwuwar shigar ta gamayyar kasashen da ke kai hare-haren jiragen sama kan mayakan ISIS a can, a cewar Shugaba Francois Hollande a yau dinnan Litini.
Da ma jiragen yakin Faransa kan shiga hare-haren da akan kai kan ISIS din a IraQi, to amma mai yiwuwa ta zama kasar farko ta Yammacin duniya, bayan Amurka, da za ta shiga tawagar kai hare-hare a Syria.
"Na umurci Ma'aikatar Tsaro cewa daga gobe ana iya kaddamar da sintirin jiragen sama a sararin saman Syria, wanda zai taimaka ma na wajen shirye-shiryen kai hare-haren jiragen sama kan 'yan Daesh," a cewar Mr. Hollande, wanda ya yi amfani da wannan lakabi na kungiyar ISIS.
Ya kuma bayyana karara cewa bai ko tunanin tura sojojin kasa zuwa Syria, inda sojojin gwamnati, da 'yan tawaye, da dakarun Al- Qaeda, da kuma 'yan ISIS - kowannensu ke yakin fadada yankinta.