Wasu hotunan da aka dauka ta hanyar yin amfani da tauraron dan adam, sun tabbatar da cewa, an lalata wani dadadden wurin ibada mai dumbin tarihi da ke birnin Palmyra na kasar Syria.
Wata hukumar Majalisar Dinkin Duniya, ta fitar da wasu hotuna da ke nuna yadda wurin ibadar ya ke kafin a lalata shi, sannan daga bisani hotunan suka nuna yadda wurin ya kasance a lalace a yau Talata.
Sai dai shugaban da ke kula da hukumar da ke adana kayayyakin tarihin kasar, Maamun Abdulkarim, ya ce, yana da tabbatacin cewa akwai sashen wurin ibadar da ba a lalata ba.
Amma ya tabbatar da cewa, lallai an samu wata babbar fashewa a wurin mai suna Temple of Bel a turance, wanda kuma ke da tarihin kasancewa tun shekaru 200 da suka gabata da kasar ta Syria ke tunkaho da shi.