Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Aljeriya Ta Kora Dubban 'Yan Ci-Ranin Nijar

Kasar Algeria Ta Mayar Da 'Yan Cirani Jamhuriyar Nijer
Kasar Algeria Ta Mayar Da 'Yan Cirani Jamhuriyar Nijer

‘Yan ci-rani 1,800 ne suka isa garin Agadez da ke Arewacin Nijar bayan da mahukuntan Aljeriya suka tasa keyarsu.

Duk da cewa akwai ‘yan kasar ta Nijar a cikin wannan ayari, amma mafi yawansu sun fito ne daga kasashen Afirka da ke Yankin Kudu da Sahara, wadanda suka shiga kasar ta Aljeriya ba bisa kan ka’ida ba.

Wasu daga cikin 'yan ci-ranin sun bayyana irin ukubar da suka sha a hannun jami'an tsaron Aljeriya kafin daga bisani a tasa keyarsu zuwa Agadez.

Kasar Algeria Ta Mayar Da 'Yan Cirani Jamhuriyar Nijer
Kasar Algeria Ta Mayar Da 'Yan Cirani Jamhuriyar Nijer

Duk da irin matakai daban-daban da hukumomin Nijar ke dauka don hana 'yan kasar tafiya ci rani zuwa wasu kasashe musamman kasashen da ke makwabtaka da Nijar, har yanzu yan kasar ba su daina ba.

Yanzu haka kasar Aljeriya ta koro wasu da suka je kasar ci rani da suka shiga ba bisa ka’ida ba, a cikin wani yanayi na kunci da wahala. Wasu daga cikin yan ci ranin sun bayyana irin wahalar da suka sha a hannun jami’an tsaron kasar Aljeriya.

Kasar Algeria Ta Mayar Da 'Yan Cirani Jamhuriyar Nijer
Kasar Algeria Ta Mayar Da 'Yan Cirani Jamhuriyar Nijer

Hukumar da ke karbar yan Nijar da aka koro daga wata kasa ta ce dukkanin yan ci ranin da Aljeriya ta koro su 1,800 suna samun kulawar da ta dace, koda yake mafi yawansu na cikin damuwa. Sulaimane Issaka jami’i ne a hukumar da ke karbar 'yan Nijar din da aka koro daga wata kasa.

Kasar Algeria Ta Mayar Da 'Yan Cirani Jamhuriyar Nijer
Kasar Algeria Ta Mayar Da 'Yan Cirani Jamhuriyar Nijer

La’akari da yadda ake samun karuwar 'yan ci ranin da ake korowa daga wata kasa, hukumar kulada 'yan ci rani ta duniya ta bullo da shirin wayar da kan 'yan ci ranin kan muhinmancin tafiya a kan ka’ida.

Saurari rahoton Hamid Mahmoud:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:19 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG