Gwamnan jihar Diffa ta Jamhuriyar Nijar Alhaji Usman Gawo ya ce kafin a kai harin Baga suna da 'yan gudun hijira daga Najerya kimanin dubu dari da hamsin. To amma yanzu adadinsu ya kai dubu dari biyu.
A cewar gwamnan jihar, sa ce ke daukan nauyin cinsu da shansu da ma kulawa da harkokin lafiyarsu sanadiyar taimakon da gwamnatin kasar Nijar da masu hannu da shuni ke bayarwa.
Mafi yawan 'yan gudun hijiran 'yan jihar Borno ne. Gwamnan Bornon Kashim Shettima ya ce suna shirin mayar da mutanen garuruwansu muddin an samu zaman lafiya amma sai gwamnati ta gama gyaran gidajensu da asibitoci da makarantu da ruwan sha tare da tanadar masu da abinci.
Su ma 'yan gudun hijiran sun ce sun fi so su koma garuruwansu.
Ga karin bayani.