Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Najeriya Sun Hallaka ‘Yan Boko Haram A Jihar Adamawa


Sojojin dake fafatawa da kungiyar Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya
Sojojin dake fafatawa da kungiyar Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya

Najeriya na cewa dakarun sojin kasar sun sami nasarar hallaka wasu yan Boko Haram a karamar hukumar Madagali, jihar Adamawa, yayin da aka kashe wani dan yakin sa kai na maharba a artabun da suka yi.

Kamar yadda bayanai suka tabbatar,yan bindiga masu tada kayar bayan na Boko Haram sun gamu da ajalinsu lokacin da suke yunkurin kai wani harin sari-ka-noke, a yankin bakin Dutse,dake karamar hukumar Madagali,wanda ke kusa da dajin Sambisa.

Wani mazauni yankin yace yan yakin sakai na maharba ne suka soma yin artabu da wadannan yan Boko Haram a bakin dutsin da suka fafata har aka kashe wani dan sakai kodayake suma maharban sun sami nasarar kai wasu yan Boko Haram lahira.

A sanarwar da hedikwatar rundunan sojin Najeriya ta fitar dake dauke da sa hannun daraktan yada labarai na rundunan, Birgediya Janar Texas Chukwu,ta tabbatar da nasarar da aka samu kan mayakan na Boko Haram a yankin na Madagali.

Da yake karin haske shi ma Yusuf Muhammad shugaban karamar hukumar Madagali ya yaba da wannan sabon yunkuri.

Kamar yadda kididdiga ke nunawa rayuka da dama ne suka salwanta baya ga wadanda ke gudun hijira sanadiyar balahirar Boko Haram musamman a arewa maso gabashin Nigeria

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:19 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG