Rundunar sojin saman Najeriya ta yi ikrarin halaka shugabannin ‘yan ta'adda tare da rugurguza masu wani sabon sansani da suka tare a ciki.
Hare-haren na baya-bayanan wadanda aka kai karkashin shirin "Operation Rattle Snake 3,” wani sabon yunkurin ne na kawo karshen ‘yan ta'addan ISWAP a Arewacin jihar Borno.
Jiragen yakin sojin saman Najeriya sun yi ta ruwan wuta a sabon babban sansanin ‘yan ta'adda na ISWAP a arewacin jihar Borno, kamar yadda hukumomin tsaro suka sanar
Kakakin rundunar Sojin saman Najeriya, Air Commodore Ibikunle Daramola, ya ce, a baya ‘yan ta'addan suna zaune ne a wani sansani da ake kira Tongule kafin daga bisani a gano wurin tare da kai masu harin.
Tsohon babban Hafsan Hafsoshin tsaron Najeriya, Air vice Marshall Al'amin Daggash, ya ce, irin wannan sabon yunkuri tabbas zai iya kai wa ga kawo karshen ayyukan ta'addanci a kasar.
Sai dai masu lura da al'amur da dama, na ganin sojojin na Najeriya ba sa tabuka wani abin a zo a gani, idan aka la'akkari da abin da ake gani a kasa.
Ko a karshen makon da ya gabata, sai da Majalisar Dokokin kasar ta tafka muhawara kan a cire shugabannin rundunonin sojin kasar saboda matsalar tsaro da ke kara ta'azzara.
Ita dai rundunar sojin kasar ta Najeriya, ta sha bayyana ire-iren wadannan nasarori da ta ke ikrarin tana samu, ba tare da an ga wani sauyi a bangaren na tsaro ba.
Saurari rahoton cikin sauti:
Facebook Forum