Masana tsaro na nuna rashin ribar bullo da zirga-zirga ta jirgin sama tsakanin Abuja da Kaduna a Najeriya don gujewa gamuwa da ‘yan ta’adda. Tuni dai a ka fara samun wannan jigila da yasa tikiti ya kai Naira dubu 25.
Abinda masanan ke cewa shi ne bullo da jigilar da masu hannu da shuni da sauran manyan jami’an gwamnati za su rika biya, zai iya sa gwamnati watsi da tsaro yadda ya dace a hanyar mota, da jirgin kasa da talakawa ke amfani da su.
Ashir Sharif na daga shugabannin kungiyoyin matasan arewa da ke ganin rashin ribar tsarin.
Hakanan kuma daga tashar jirgin saman Kaduna zuwa cikin gari ma ‘yan ta’addan na iya fakewa don cutar da jama’a.
Masani kan zirga-zirgar jiragen sama Kaftin Bala Jibrin bai ga laifin sabuwar hanyar ba, don ya ce ba laifi ba ne in kamfanonin jirage masu zaman kan su, su ka shiga harkar don kasuwanci.
Zuwa yanzu dai wani kamfani daya ne ya bude teburin sayar da tikitin zirga-zirgar saman daga Abuja zuwa Kaduna.
A saurari rahoto cikin sauti daga wakiliyar Muryar Amurka Hauwa Umar.
Facebook Forum