Matakin da hukumar zaben Najeriya ta dauka na soke rejistar jam’iyyu marasa tasiri 74 ya janyo martani inda wasu ke da ra’ayin cewa da hukumar ta tsaurara matakin rage jam’iyyun su dawo 5 daga 18 da ta bari da rejistar.
Shugaban hukumar zaben Farfesa Mahmud Yakubu ya ce doka ta ba wa hukumar damar soke jam’iyyar da ta saba ka’idar rajista.
Tun kammala zaben 2019, cibiyar bunkasa damokradiyya ta ce jam’iyyun sun yi yawa kan takardar kada kuri’a, dalilin da ke haddasa wahalar tsarin zabe.
Mai sharhi kan lamuran siyasa Ansa Dan Nayaba ya yi maraba da soke jam’iyyun da ya ce tamkar ‘yan amshin shatar manyan jam’iyyu ne.
Amma kuma shugaban jam’iyyar NDLP da aka soke Alhaji Umaru Mai Zabura ya musanta batun zama ‘yan baranda ga manyan jam’iyyu.
Tun dawowa dimokaradiyyar Najeriya a 1999 zuwa yanzu jam’iyya daya ce ta lashe zaben tarayya ta yi mulki na tsawon shekaru 16 inda hadakan jam’iyyun adawa wajen 4 su ka game da kafa APC su ka amshi 2015.
A saurari rahoto cikin sauti daga Abuja.
Facebook Forum