Kwamishanan yankin Mandera Fredrick Shisia ya shaidawa Muryar Amurka Sashen Somali jami'an tsaron na kyautata zaton motar na dauke da nakiyoyi kafin su harbe mutane biyun dake cikinta.
To saidai shaidun gani da ido sun ce mutanen da aka kashe fararen hula ne kuma basa dauke da makami. Sun kara da cewa wadanda suka jikata mutane ne dake wucewa.
A wata sabuwa kuma mazauna garin sun ce ana gudanar da wani babban bincike a yankin na Madera yau Litinin biyo bayan harin da aka kai har ya yi sanadiyar mutuwar jami'an 'yansanda biyu a wajejen Lafey jiya Lahadi.
To saidai mayakan sa kai na kungiyar al-Shabab tuni suka dauki alhakin kai harin da ya rutsa da 'yansandan.
Mayakan sa kai na kungiyar Islama ta al-Shabab sun sha kai hare-hare cikin kasar Kenya tun lokacin da sojojin kasar suka shiga Somaliya da nufin yakar al-Shabab a watan Oktoban shekarar 2011..
A wani harin da ya fi muni mayakan al-Shabab sun bindige dalibai 148 a jami'ar Garissa dake tsakiyar kasar Kenya watan Afrilu da ya gabata.