Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mayakan al-Shabab sun kai hari kan dakarun kungiyar Afirka


Sojojin Uganda na dakarun kungiyar kasashen Afirka
Sojojin Uganda na dakarun kungiyar kasashen Afirka

Shaidu a yankin Gedo da ke Somalia, sun ce mayakan Al Shabab, sun kai hari akan a wani sansanin dakarun hadin gwiwa na Afrika da ke garin El Adde, mai tazarar kilomita 60 kudu da Garbaharrey, babban birnin yankin.

An kai harin ne da sanyin safiyar yau Juma’a bayan da wani dan kunar bakin wake ya tarwatsa kansa, sannan wasu ‘yan bindiga suka yi arangama da wasu dakarun kasar Kenya da aka jibge a sansanin.

Kungiyar ta Al shabab dai ta yi ikrarin ta kashe da yawa daga cikin dakarun, kuma ta karbe ikon sansanin, sai dai rundunar hadin gwiwar, wacce ake wa lakabi da AMISOM, ba ta tabbatar da wannan ikrari ba.

Amma wasu mazauna yankin sun ce lallai mayakan na Al shabab sun karbe ikon garin sannan sun daga tutarsu, yayin da suka kuma ce mayakan sun karbe wasu makamai a cikin wata mota mallakar dakarun hadin gwiwar.

Ko a watannin Yuni da Satumbar shekarar da ta gabata ma, mayakan na Al Shabab sun kai wani hari makamancin wannan, inda suka halaka da dama daga cikin dakarun hadin gwiwar na AMISOM.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG