A cikin wani sabon rahoto da hukumar ta sake fitarwa jiya Talata, tace keta 'yancin Bil'Adaman ya zama ruwan dare gama duniya a tsakankanin hukumomin tsaron, kuma an hada baki wajen aiwatar da shi".
Masu bincike sun ce sun sami labarin sau da yawa babu hujja ta kwarai haka za'a siddan za'a kamo mutane da ake zargi, sai a tsare su na sa'o'i wasu kwanaki a wurare da suke cike makil da fursinoni kuma cikin munanan yanayi da basu misaltuwa.
Haka nan rahoton ya ci gaba da cewa akwai zargin gallawa mutanen, da duka, da amfani da wutar lantarki a gallazawar, da kuma cusa fursinonin cikin ruwa shigen nustar da su. Wasu sai a makala su daga kan itatuwa suna reto, wasu kuma a saka su cikin kwari ko cinnaka.
Rahoton yace wadanda ake kamawa galibi 'yan kasar Somalia da Musulmi aka fi aunawa. 'Yan'uwa ko dangi wadanda suke neman bayanai daga hukumomi dangane da 'yanuwansu da suka bace basa samun wani taimako daga hukumomin kasar.
Hukumar tace, kodashike ta fahimci "kalubale iri iri" da gwamnatin Kenya take fuskanta a yaki da take yi da ta'addanci da mutane masu tsatsauran ra'ayi, duk da haka tilas ne ta gudanar da wannan yaki kan hanyoyi da doka ta tanadar da kuma mutunta 'yancin Bil'Adama da hukumomin duniya suka amince da su.