Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gobara Ta Hallaka Wasu Daliban Makarantar ‘Yan Mata Ta Jogana


Gobara Na Ci
Gobara Na Ci

Gobara ta tashi a makarantar 'yan mata ta garin Jogana a jihar Kano har ta hallaka tare da jikkata dalibai.

An sami rasuwar dalibai mata guda bakwai na makarantar kwana ta ‘yan mata da ke garin Jogana, sai kuma wasu dalibai guda asirin da biyar.

Haka kuma a halin da ake ciki gwamnatin jihar Kano ta bada sanarwar rufe makarantar har sai an gyara tare da binciken musabbabin gobarar.

Mataimakin gwamnan jihar Kano Farfesa Hafizu Abubakar kuma kwamishinan ilimi na jihar shine ya bada wannan umarni tare da jajantawa iyalan wadanda abin ya shafa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:33 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG