Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fara Shari’ar Wasu Sojoji Da Ake Zargi Da Aikata Laifi A Jamhuriyar Nijar


Shugaba Macron Ya Kai Ziyarar Bangirma Ga Sojojin Nijar Da Suka Mutu (Mun yi amfani da wannan hoto don nuna misali ne, wadannan ba su ne wadanda ake tuhuma ba)
Shugaba Macron Ya Kai Ziyarar Bangirma Ga Sojojin Nijar Da Suka Mutu (Mun yi amfani da wannan hoto don nuna misali ne, wadannan ba su ne wadanda ake tuhuma ba)

Laifukan da ake tuhumar sojojin sun hada da zargin yin fyade, batar kayan aiki sata da kuma arcewa daga aikin na soja.

Kotun hukunta laifikan soja ta fara zamanta a birnin Yamai, Jamhuriyar Nijar, domin shari’ar wasu sojojin kasar da ake zargi da aikata ba daidai ba.

Sai dai masu rajin kare hakkin dan adam sun fara jan hankula akan maganar daukan matakan mutunta ‘yancin dan adam a yayin wannan zama.

Kimanin shari’a 13 ne kotun ke saran dubawa a yayin wannan zama da za a shafe mako 1 ana gudanarwa a mashara’antar dake da ofishi a wannan karon a cibiyar horar da jami’an tsaron jandarma dake n’guwar Koira Tegui ta birnin yamai.

A yayin bukin bude wannan zama Janar Mahamadou Abou Tarka dake daya daga cikin mambobin wannan kotu ya yi karin haske akan batutuwan da za a maida hankali akansu.

Ya ce yunkurin yiwa kasa barazana da ake zargin kanal Zanguina da sauransu na daga cikin batutuwan da wannan zama zai duba.

Sai kuma batun da ya shafi zargin yin fyade ga wata yarinya mai shekaru 14 sannan akwai shara’a biyar da suka shafi zargin batar da kayan aikin soja da kuma wasu guda biyu da suka shafi zargin sata da shara’a biyu na zargin arcewa daga aikin soja ba akan ka’ida ba.

Sai wani case na aikata laifi a bainar jama’a cikin yanayin maye da kuma case 1 da ya shafi zargin damfara.

Jami’an kare hakkin dan adam sun yaba da wannan yunkuri to amma kuma sun yi jan hankula akan maganar kiyaye ‘yancin mutanen da ake zargi dai dai da abubuwan da dokokin kasa da kasa suka yi tanadi.

Alhaji Nassirou Saidou shi ne shugaban kungiyar Voix des sans Voix,da yake magana akan tsarin zaman kotun ta Tribunal Militaire shugabanta mai shara’a Alio Daouda ya ba da tabbacin komai zai gudana akan ka’ida.

Yace za ku gani a yayin wannan zama duk wanda ake tuhuma zai amsa tambayoyi da kansa idan kuma ya na da lauya zai iya kare shi haka kuma ya zama dole ta yi tanadin lauya ga duk wanda ba shi da lauyan da zai kare shi.

Kamar yadda aka saba a wannan jikon ma jama’a na da ‘yancin halartar zaman shara’ar domin su shaidi yanayin da abubuwa zasu wakana.

XS
SM
MD
LG