Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Amurka Sun Kammala Janyewa Daga Birnin Yamai


United States Niger Troops
United States Niger Troops

Sojojin Amurka sun kammala janyewa daga sansaninsu da ke Yamai babban birnin jamhuriyar Nijar, kuma za su fice gaba daya daga kasar ta Agadez kafin cikar wa'adin ranar 15 ga watan Satumba da shugabannin sojan kasar suka sanya, a cewar kasashen biyu ranar Lahadi.

A watan Maris ne shugabannin sojan Nijar suka soke yarjejeniyar hadin gwiwar soja da suka kulla da Washington, bayan da suka kwace mulki a watan Yulin 2023.

Amurka na da sojoji kusan 650 a Nijar a zaman wani bangare na kokarin yaki da ‘yan ta’adda a kasashen yankin Sahel da yawa a yammacin Afirka, ciki har da wani babban sansanin jiragen sama marasa matuki a kusa da Agadez.

"Ma'aikatar tsaron Nijar da ma'aikatar tsaron Amurka sun sanar da cewa an kammala janye sojojin Amurka da kayan yaki daga sansanin 101 na Yamai."

A yammacin ranar Lahadi ne jirgin karshe dauke da sojojin Amurka ya bar birnin Yamai.

Dakarun Amurka 950 aka girke a kasar, kuma sojoji 766 ne suka bar Nijar tun bayan da sojojin kasar suka ba su umarnin barin kasar, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya sami bayani a wurin wani biki da aka gudanar a sansanin, wanda ya samu halartar babban hafsan sojan Nijar Maman Sani Kiaou da Janar Kenneth Ekman na Amurka.

"Sojojin Amurka yanzu za su mayar da hankali kan barin sansanin sojan sama na 201 a Agadez," a cewar sanarwar, ta kuma jaddada cewa za a kammala janye sojojin zuwa ranar 15 ga watan Satumba kamar yadda aka tsara.”

Tuni dai dama Nijar ta ba da umarnin a janye dakarun kasar Faransa, tsohuwar kasar da ta yi wa Nijar mulkin mallaka kuma daddadiyar kasar kawancenta, sannan ta karfafa alaka da Rasha wacce ta samar wa Nijar masu horar da sojoji da kayan aiki.

A ranar Asabar, ma'aikatar tsaron Jamus ita ma ta ce za ta kawo karshen ayyukanta a sansanin sojanta da ke Nijar zuwa ranar 31 ga watan Agusta, bayan da suka samu matsala a tattaunawa da shugabannin sojoji.

An samu makamancin wannan sauyi a kasashen Mali, da Burkina Faso da ke makwabtaka da Nijar, wadanda suma ke karkashin mulkin shugabannin soja suna kuma fuskantar tashin hankalin kungiyoyin ‘yan ta’adda.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG