Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojoji Sun Rutsa Da Makiyayan Da Suka Kona Wani Kauye A Jihar Adamawa


Hafsan Hafsoshin Sojojin Najeriya Janar Buratai
Hafsan Hafsoshin Sojojin Najeriya Janar Buratai

Sojojin dake atisayin tseren bera a wasu jihohin dake tsakiyar Najeriya sun kai dauki a karamar hukumar Numan cikin jihar Adamawa inda suka kashe makiyaya goma cikin wadanda suka kona garin Gomba kurmus

Wata sanarwa daga hedkwatar rundunar sojojin Najeriya dake Abuja da ta samu sanya hannun sabon kakain sojojin Birgediya Janar Chukwu ta ce sojojin da suke atisayin tseren bera a jihohin dake tsakiyar Najeriya sun samu kiran neman dokin gaggawa daga karamar hukumar Numan dake jihar Adamawa.

Kiran neman dokin gaggawan ya biyo bayan harin da wasu makiyaya suka kai kauyen Gomba ne. Kafin sojojin su isa kauyen makiyayan sun kona garin kurmus.

Lamarin ya sa sojojin su bi sawun makiyayan inda suka samu cafke guda shida a kauyen Gargiji yayinda suke kokarin tserewa. Ana cikin haka ne kuma makiyayan suka nuna turjiya al'amarin da ya sa sojojin suka bude wuta har suka kashe guda goma a cikinsu.

Baicin kashe makiyaya goma, sojojin sun samu bindigogi da harsashai da adduna daga makiyayan.

Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:00:59 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG