Hadakar ‘yan adawar kasar Mali sun ce jami’an tsaro sun kulle wasu shugabannin masu shirya zanga-zangar kin jinin gwamnati su biyu sun kuma kai samame a shelkwatar ‘yan adawar ranar Asabar 11 ga watan Yuli bayan wata mummnar zanga-zanga da aka yi a kasar.
Guguwar zanga-zangar ta dan lafa inda aka ga gungun wasu masu zanga-zangar suna toshe hanyoyi da tayoyi da kuma katakai don hana ababen hawa wucewa zuwa gundumomin birnin Bamako da yawa, ko da yake adadin masu zanga-zangar ya ragu idan aka kwatanta da wadanda suka fita zanga-zanagar ranar Juma’a 10 ga watan Yuli.
Hadakar ‘yan adawar da ake kira M5-RFP ta ce an kulle Choguel Kokala Maiga da Mountaga Tall, manyan shugabannin masu shirya zanga zangar a ranar Asabar tare da wasu ‘yan gwagwarmaya. Wani jagoran masu zanga-zangar, Issa Kaou Djim, shi ma an kama shi ranar Juma’a
Facebook Forum