Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Zanga-zanga a Mali Sun Ce Ba Gudu Ba Ja Da Baya


Masu zanga-zanga a Mali
Masu zanga-zanga a Mali

Dubban mutane ne suka sake fitowa a birnin Bamako na kasar Mali domin kira ga shugaba Ibrahim Boubacar Keita da ya sauka daga kan mukaminsa.

Hakan na nuni da cewa dukannin kokarin da shugabannin kasashen waje suke ta yi domin kawo karshen rikicin siyasar kasar ya cutura.

Wata gamayya mai suna M5-RFP ce take shirya zanga-zangar da suka mamaye kasar a watan Yuni sakamakon żargin gwamnatin da cin hanci da rashawa da kuma rashin cancanta.

Tun da aka harbe masu zanga-zanga 11 a watan Yuli ne Lamarin ya kara kazanta.

Zanga-zangar Mali
Zanga-zangar Mali

Shugabbanin duniya na fargabar cewa idan aka ci gaba da rikici da rashin zaman lafiya a kasar, hakan zai iya kawo cikas ga kokarin da ake yi na dakile 'yan ta'adda a kasar ta Mali.

Shugaba Keita ya sa ran cewa kokarin sulhu da 'yan hamayya tare da sa bakin shugabannin duniya zai rage tsanar da ake masa, amma bisan ga dukkan alamu ko a jikin masu zanga-zangar.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG