Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rikicin Siyasar Mali Na Kara Ta'azzara


Shugaban kasar Mali, Ibrahim Boubacar Keita
Shugaban kasar Mali, Ibrahim Boubacar Keita

Babbar jam’iyyar adawa a Mali ta yi watsi da wani shiri da masu shiga-tsakani na yankin suka gabatar a kokarin da ake yi na kawo karshen rikicin siyasar kasar.

Masu fafutukar da ake kira “June 5 Movement,” sun yi watsi da shirin da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ta ECOWAS ta gabatar a ranar Lahadi, wanda ya nemi shugaban kasar Boubacar Keita da ya kafa gwamnatin hadin-kai tare da bangaren ‘yan adawa.

A baya Shugaba Keita ya mika wuya ga wata bukata da ‘yan adawa suka gabatar, inda suka nemi da ya rusa kotun kundin tsarin mulkin kasar.

Amma kungiyar ta June 5 movement, ta ci gaba da tsayawa tsayin-daka kan sai shugaba Keita ya yi murabus daga mukaminsa.

Wadannan ala'amura na faruwa ne yayin da kasar ta Mali wacce ke yammacin Afirka take fama da matsalolin rikice-rikice, komadar tattalin arziki da kuma hare-haren da ‘yan ta’adda suka kwashe shekara takwas suna kai wa a tsakiyar kasar.

Baya ga wadannn matsaloli, akwai kurar da ke yunkurin tasowa dangane da sakamakon zaben ‘yan majalisu da aka yi wanda har yanzu ake rikici a akai.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG