Sai dai ba a samu labarin mutuwa ko jikkata a wannan sumame da sojojin suka kai karshen makon nan a unguwar Gidan Igwai ba.
Mai magana da yawun birged din, Kyaftion Yahaya Musa, yace sun kama 'yan bindigar da ake kyautata zaton 'yan Boko Haram ne a wannan sumame, amma kuma bai bayyana yawansu ba.
Kakakin yace sun kai wannan sumame ne a bayan wasu bayanai na leken asiri da kuma tallafin jama'ar gari wadanda suka ga alamun 'yan bindigar a wannan unguwa. Yace sun sanya idanu sosai kan abubuwan dake wakana a saboda fargabar cewa 'yan bindigar dake tserewa daga matakan soja a jihohin Borno da Yobe, wasunsu su na neman wuraren buya a Sokoto.
'Yan makonni kadan da suka shige ma, jami'an tsaron a Sokoto sun kai farmaki kan wata maboyar 'yan Boko Haram a birnin na Sokoto.