Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

JTF Ta Yi Gargadi Cewa Boko Haram Tana Kulla Kai Hari A Maiduguri


Wani sojan Najeriya cikin mota mai sulke a Maiduguri, Jihar Borno
Wani sojan Najeriya cikin mota mai sulke a Maiduguri, Jihar Borno

Rundunar JTF ta yi gargadin cewa 'ya'yan Boko Haram su na kulle-kullen kai hari daga yanzu zuwa lokacin bukukuwan Sallah na Edi el-Fitr

Rundunar tsaron hadin guiwa ta dakarun Najeriya a yankin Arewa maso gabashin Najeriya, ta gargadi mutanen Jihar Borno cewa 'ya'yan kungiyar Boko Haram su na kulle-kullen kai manya-manyan hare-hare a cikin Maiduguri da kuma wasu sassa na Jihar daga yanzu, da kuma lokacin da ake bukukuwan karamar Sallah ta Eid el-Fitr.

A cikin wata sanarwar da Leftana-Kanar Sagir Musa, kakakin rundunar ta JTF a Maiduguri ya bayar, an roki jama'a da su kula sosai da dukkan abubuwan da suke faruwa a kewaye da su, su kuma yi hattara a wannan lokacin.

Haka kuma, an shawarci jama'a a ciki da wajen Maidugurin, da su kai rahoton duk wani abinda suka ga yayi dabam ga jami'an tsaro mafi kusa da su, musamman wuraren da ake bincike. Musamman kuma, ana son jama'a su gaggauta kai rahoto idan sun ga an ajiye wata jaka ta laida ko wani buhu a inda jama'a ke taruwa ko wucewa.

Kanar Sagir Musa yace koda yake an sassauto da dokar hana fita waje ta koma daga karfe 11 na dare zuwa 6 na safiya, ana ci gaba da gudanar da ayyukan bincike a duk tsawon dare domin tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin jama'a, tare da karfafa irin nadsarorin da rundunar tsaro ta samu a yaki da ta'addanci.
XS
SM
MD
LG