A lokacin da yake hira ta wayar tarho da VOA Hausa, mutumin mai kiran kansa Marwana, yace akwai wadanda suka bayyana shakkar sahihancinsa, kuma tun kafin a kai wannan harin, sai da ya sanar da wadanda ke shakkar maganarsa cewa za a kai shi. Yace dalili shi ne ana samun kwan-gaba kwan-baya a kan maganganun da suke yi, shi ya sa suka dauki wannan matakin.
Sai dai yayi gargadin cewa ba su kadai ne 'ya'yan kungiyarsu suke kai irin wadannan hare-haren ba, domin akwai masu fakewa da shi domin tabbatar da cewa ba a toshe musu hanyoyin samu ba.
A kan ko wannan batu na harin Sabon Gari koma-baya ne tunda shi da bakinsa yayi alkwarin cewa ba za a sake samun hakan ba, sai mutumin yace ba koma-baya ba ce domin kashedi ne.
Babu wata hanya ta dabam, ko wata kafa mai zaman kanta, ko ta tsaro, da ta gaskata kalamu da kuma ikirarin da shi wannan mutumi yake yi.