Cardinal Onaiyekan yayi wannan furucin ne a wajen wata liyafar buda-bakin hadin guiwa a tsakanin Musulmi da Kirista, wadda Cibiyar Zantawar Addinai ta shirya a Masallacin Unguwar 'Yan Majalisa dake Abuja.
Onaiyekan yace rikice-rikicen dake faruwa a yankin arewacin Najeriya, sun kawo sabani sosai a tsakanin Musulmi da Kirista, a saboda haka ya kamata masu rinjaye na wadannan addinai da suke hulda tare da mutunta juna su kara mikewa tsaye domin yayata fahimtar juna.
Babban fadan na 'yan Katolika a Abuja, yace ba majami'u kawai ake kai wa hari ba, har da masallatai, ba fastoci kawai ake kashewa ba, har da limamai, don haka wannan fitina kowa ta shafa.
Limamin Masallacin na Unguwar 'Yan Majalisa, Sheikh Nuru Khalid, yace sun gayyaci matasa Kirista da Musulmi ne domin da matasa ake amfani wajen haddasa fitina a kasa, su kuma su na son suyi amfani da matasan domin dasawa da karfafa fahimtar juna da mutunta addinan juna don kara dankon zumunci.
Yace ya kamata hukuma ta tabbatar da cewa dandalin wa'azi, bai zamo dandalin yada gaba ko kiyayyar juna ba.