Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sinead O'Connor, Ta Mutu Tana Da Shekara 56


Sinead O'Connor
Sinead O'Connor

Sinead O'Connor, mawakiyar kasar Ireland, mai tsaurin ra’ayi da aka fi sani da  murya mai amo, da kuma wakar da ta yi a 1990, da ake kira "Nothing Compares 2 U", ta mutu tana da shekara 56, kamar yadda kafafen yada labarai na Ireland suka sanar jiya Laraba..

"Da bakin ciki muka sanar da rasuwar masoyiyarmu Sinead. 'Yan uwanta da abokanta sun yi matukar bakin ciki kuma sun nemi a ba su sirri a wannan mawuyacin halin da su ke ciki," in ji RTE a wata sanarwa daga dangin mawakiyar.

Har yanzu dai ba a a san sanadiyar mutuwarta ba.

Sinead O'Connor
Sinead O'Connor

Ta shahara sosai ne saboda ra'ayoyinta na zahiri game da addini, jima'i, goyon bayan ‘yancin mata da kuma yake-yake.

An haifi Sinead Marie Bernadette O'Connor a wata unguwar masu arziki a Dublin, a ranar 8 ga Disamba, 1966. A cikin tarihinta na 2021, O'Connor ta ce mahaifiyarta, wacce ta mutu a wani hatsarin mota a 1985, ta ci zarafinta da ta ke yarinya..

Sinead O'Connor
Sinead O'Connor

Sinead, wadda ta yi aure sau hudu, kuma wadda aka nada ta a matsayin limamiyar coci a shekarar 1999 ta wata kungiyar Katolika da ta balle ta musulunta a shekarar 2018 inda ta canza sunanta zuwa Shuhada Sadaqat, duk da cewa ta ci gaba da yin waka da sunan Sinead O'Connor.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG