Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Duniya Sun Kasa Hada Kai Wajen Yaki Da COVID-19


Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya(MDD) ya fada a wata hira da ya yi da BBC cewa bala’i ne ganin shugabannin duniya sun gaza hada kai wurin yaki da COVID-19, ta hanyar da ta dace.

Antonio Guterres ya ce kowace kasa ta yiwa kanta tsari ne, kasashe daban daban suna tunkarar yakin ne ta fuskoki da dama da kuma dabaru mabambanta kuma haka ya baiwa cutar damar bazuwa.

Shugaban na MDD ya ce lallai an gaza wurin shugabanci, a wannan yaki da cutar. Kan haka ne ya yi kira ga manyan kasashen duniya da su hada kai su bullo da tsari daya don taimakawa sauran kasashen.

MDD ta kiyasta kashi takwas cikin dari na al’ummar duniya, da zasu kai mutum miliyan 500 ne zasu fada cikin talauci ala tilas kafin karshen shekara saboda irin barnar da cutar tayi.

Cutar coronavirus na ci gaba da kara ta’azzara a fadin duniya, kamar yadda cibiyar John Hopkins mai sa ido a kan cutar ta fada da safiyar ranar Juma’a, cewa akwai mutum sama da miliyan uku da dubu 200 da suka kamu da cutar kana, wasu dubu 233 suka mutu.

Har ya zuwa yanzu dai Amurka ce kan gaba da mutane sama da miliyan suka kamu da COVID-19 kana, wasu sama da dubu 63 suka mutu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG