Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

COVID-19 Ta Hana Yara Biliyan 1.5 Zuwa Makaranta


Kungiyoyin kare hakkokin bil’adama sun ce ta yi wu yara ne annobar coronavirus za ta fi shafa, duk da cewa cutar ta fi kama galibin masu manyan shekaru.

An kiyasta cewa yara biliyan 1.5 a fadin duniya ba sa zuwa makaranta.

Annobar kuma na shafar yara ta hanyoyi da yawa, dubbansu sun zama marayu sanadiyyar cututtukan da coronavirus ke janyowa.

“Yara da yawa za su rasa iyayensu," a cewar Jo Becker na kungiyar kare hakkokin bil’adama ta Human Rights Watch.

Ya kara da cewa, “mun ga abin da ya faru a lokacin annobar Ebola, da kuma a misali cutar da ke karya garkuwar jiki ta HIV a yankin kasashen Afrika da ke kudu da Hamadar Sahara."

A cewar Becker, "lamarin ya jefa yaran da suka zama marayu cikin hadarin fadawa tarkon masu safarar yara don karuwanci, yin aikin karfi da kuma wasu abubuwan da ba su dace ba."

Wani rahoton kungiyar ‘yan kwadago ta kasa-da-kasa da aka fitar a kwanan nan, ya yi gargadin cewa, ta yi wu mutum miliyan 200 su rasa ayyukansu sakamakon annobar coronavirus.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG