Kasashen New Zealand da Italiya sun yi shelar matakansu na sassauta killacewa ta dakile yaduwar cutar coronavirus.
Hakan na zuwa ne a yayin da Firai ministan Burtaniya Boris Johnson, wanda ya koma bakin aiki jiya Litinin bayan murmurewa daga cutar COVID-19, ke cewa zai yi wuri a sassauta takaita harkoki a Burtaniya a yanzu.
Johnson, wanda ya yi jawabi a harabar ofishinsa da ke Downing Street, ya ce ya fahimci matsuwa da kuma zullumin jama’a.
Amma ya ce muddin aka sassauta takaita harkoki a yanzu, za a fuskanci kasadar abin da ya kira, “sabbin mace-mace da barkewar cutar” wanda zai ma dada gurgunta tattalin arzikin kasar.
“Na ki in salwantar da dukkan fama da sadaukarwar da mutanen Burtaniya suka yi, da kasadar fuskantar wata barkewar annobar a karo na biyu, da rasa rayuka da dama da kuma buwayar bangaren kiwon lafiya na Burtaniya,” a cewarsa.
Johnson ne shugaban kasa na farko da ya kamu da cutar COVID-19, ya kuma shafe kwanaki a dakin masu bukatar matukar kulawa a asibiti, inda ya yi ta fama da cutar.
Facebook Forum