Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon, yace ya damu sosai da fadan dake kara yin tsanani a tsakanin sojojin Arewaci da na Kudancin Sudan, yayin da yankin kudu ke shirin zamowa kasa 'yantacciya a wata mai zuwa.
A cikin wata sanarwar da kakakinsa ya bayar jiya laraba, Mr. Ban yayi kiran da a kawo karshen fadan da ake yi a Jihar Kordofan ta Kudu, inda mutane dubu 60 suka gudu daga gidajensu a cikin kwanaki goma da suka shige domin gujewa fada. ya roki dukkan sassan da su kyale Majalisar Dinkin Duniya ta shiga yankin ba tare da tsangwama ba domin tabbatar da tsaron lafiyar ma'aikatanta, tare da samar da agaji ga mutanen yankin.
Jami'ai sun ce a yau alhamis wata tawagar hadin guiwa ta Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Tarayyar Afirka zata doshi Jihar Kordofan ta Kudu a Sudan a wani yunkurin kawo karshen kazamin fadan da ake gwabzawa a can.
A halin da ake ciki, wani kakakin sojojin Kudancin Sudan, Philip Aguer, yace sojojin Arewaci da Kudancin Sudan sun yi musanyar wuta jiya laraba a bakin kogin Bahr al-Arab, a lokacin da a cewarsa sojojin atrewaci suka yi kokarin ketare wata gadar da ta ratsa kogin. Amma kuma kamfanin dillancin labarai na Associated Press ya ambaci wata mai magana da yawun Majalisar Dinkin Duniya tana fadin cewa sun samu rahotannin da suka saba da juna a kan kowane bangare ne a tsakanin sassan biyu yayi kokarin ketare gadar.
Ba a dai ji ta bakin jami'an Arewacin Sudan kan wannan lamarin ba har yanzu.
Wannan sabon tashin hankali yana zuwa a daidai lokacin da Kungiyar Tarayyar Kasashen Afirka ta ke gudanar da wani taron neman sulhu a birnin Addis Ababa bisa fatar shiga tsakani domin sasanta Arewaci da Kudancin Sudan.