Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nasir Idris Na Jam’iyyar APC Ya Lashe Zaben Gwamnan Jihar Kebbi


Dakta Nasir Idris
Dakta Nasir Idris

Jami’in tattara sakamakon zabe ya ayyana Idris a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Kebbi ranar Lahadi 16 ga watan Afirilu.

Dan takarar jam'iyyar APC a jihar Kebbi Dakta Nasir Idris (Kauran Gwandu) ya lashe zaben gwamna da aka kammala ranar Asabar 15 ga watan Afirilu, 2023.

Jami'in tattara sakamakon zabe farfesa Yusuf Sa'idu na jami’ar Usman Danfodio da ke Sokoto ne ya gabatar da sakamakon zaben.

Dakta Nasir Idris
Dakta Nasir Idris


Yace Dakta Nasir Idris ya samu kuri'a 409,225 inda ya doke dan takarar jam'iyyar PDP Manjo Janar Aminu Bande mai ritaya wanda ya zo na biyu da kuri'a 360,940. Hakan nan nufin kuri’u 48,285 ke tsakanin ‘yan takarar.

Wannan sakamakon dai ya nuna cewa jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta kara samun kujerun gwamna.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG