Wasu daga cikin ‘yan kwamitin majalisun Tanzaniya game da ayyukan al’umma sun yi murabus, tare da bukatar shugaban majalisar da ya gudanar da bincike mai zurfi kan zargin da ake yiwa wasu daga cikin ‘yan majalisar na cewa suna karbar cin hanci da rashawa daga hannun wasu masana’antu na gwamnatin kasar.
Yawancin yan majalisun da ake zargi sun fito ne daga jam’iyyar shugaban kasa John Magufuli ta CCM. ‘yan Tanzaniya dai na cewa wannan zargi da ake yiwa ‘yan majalisun gaskiya ne, yana kuma rushe kokarin shugaban na yaki da cin hanci da rashawa a ma’aikatu, kamar yadda yayi alkawari kafin zaben kasar.
Amma kuma ministan yada labarai Nape Nnauye, yace ‘yan majalisun da ya gana da su sun musunta karbar cin hanci da rashawa. Nnauye, wanda yake shima dan majalisa ne yace shugaban kasa ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen ganin ya dauki mataki ga duk wanda aka samu da wannan laifin.
Kafar yada labaran kasar ta fitar da rahotan cewa kamfanin inshora na NHIF ya yiwa ‘yan majalisun da ke cikin kwamitin ayyukan jama’a tayin jaka cike da kudi. Rahotan na cewa