Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, yayi kira ga hukumomin kasa da kasa da su hada kai wajen tunkarar babbar matsalar da ake fama da ita a duniya ta ‘yan gudun hijira.
Erdogan yayi wannan kira ne a jiya Litinin, lokacin taron kolin kwanaki biyu na Majalisar Dinkin Duniya ko MDD a Istanbul, don shimfida ingantattun hanyoyin tunkarar matsaloli masu alaka da alamuran 'yan gudun hijirar da suka gujewa yaki a Siriya da Iraqi zuwa Turkiyya.
Masu fashin baki sunce kasancewar yan gudun hijira Miliyan 3 a Turkiyya, hakan ya mayar da kasar wadda tafi kowacce wajen karbar yan gudun hijira a duniya, MDD tace ba a taba ganin mummunar matsalar yan gudun hijira ba tun yakin duniya na biyu.
Duk da cewar ana tambaya a kan ko taron kolin zai iya haifar da sakamako mai kyau, babban sakataren MDD Ban Ki-moon, yayi kira ga wakilai da shugabannin kasashe sama da 60 cewa “mu kuduri aniya yanzu, ba wai kawai mu kare rayukan mutane ba, amma mu baiwa mutane damar samun rayuwa mai inganci da walwala.”