Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Turkiya ya zargi kasashen yammacin turai da rashin taimakawa kasarsa


Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan
Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan

Shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan yana zargin shugabannin kasashen yammacin turai da kasa taimakawa kasarsa a yakin da ta ke yi da masu tsatstsauran ra'ayin addinin musulunci, wato ISIS a arewacin kasar Syria

Shugaba Erdogan yace kasashen yammacin turai sun gaza ba gwamnatinsa taimako a fafatawar da su keyi da da mayakan sa kai na kungiyar Islama cikin kasar ta Turkiya.

Yace "sun barmu muna fafatawa da kungiyar ISIS, kungiyar dake kashe mana mutane ta yin anfani da masu kunar bakiin wake dake tada bamabamai da kuma wadanda suke shigowa kasar ta kan iyaka a garin Kilis" Shugaban ya yi furucin ne jiya Lahadi a birnin Istanbul.

Yayi kalamun nasa ne kwana guda bayan mahukuntar kasar sun sanar cewa ruwan bamabamai da kasar tayi akan arewacin Syria ya hallaka mayakan ISIS 55 a matsayin wani martani kan rokoki da kungiyar ISIS ta dinga jefawa kasa har tsawon makonni biyu da suka kashe mutane fiye da ishirin kusa da Kilis.

Majiya daga rundunar sojin kasar ta ambato kamfanin labarai na Reuters yana fada ranar Asabar cewaTurkiya ta auna bamabaman ne kan yankin Aleppo da ya yi fama da samun hare-hare. Ruwan bamabaman na Turkiya sun rugurguza wuraren da ISIS ta kafa rokoki da kuma motoci uku.

Zargin baya bayan nan na Erdogan ya nuna dangantaka ta yi tsami tsakanin gwamnatinsa da Tarayyar Turai. Dama Tarayyar Turai ta bukaci Turkiya ta yiwa dokar yaki da ta'adanci gyran fuska saboda tana ganin ana anfani da dokar ne wurin musgunawa masu adawa da shugaban kasar.

Saidai shugaban ya hakikance kasar dake fuskantar barazana daga 'yan tawayen kurdawa da ISIS na bukatar ta karfafa dokokinta ba yin sassauci ba.

XS
SM
MD
LG