Jam'iyyar dake mulkin kasar Turkiya ta zabi Binali Yildrim wani mukarrabin shugaba Reccep Tayyip Erdogan a zaman shugaban jam'iyyar kuma watakila shi za'a ba mukamin Firayim Ministan kasar.
Mr Yildrim, shi ne ministan harkokin sufurin kasar kuma yana daya daga cikin wadanda suka kafa jam'iyyar Justice and Development.
Zai maye gurbin Firayim Minista Ahmet Davutoglu wanda jiya Lahadi yayi murabus a hukunce, bayan da yayi ta fuskantar sabanin ra'ayi tsakaninsa da shugaba Erdogan.
Mr. Yildrim dan shekara sittin da haihuwa yayi takarar shugabancin jam'iyyar ba tare da hamayya ba, kuma ana sa ran zai goyi bayan burin shugaba Erdogan na yiwa kundun tsarin mulkin kasar kwaskwarima.
A jawabin da ya gabatar kafin a zabeshi, Mr. Yildrim ya yi alkawarin yiwa shugaban kasar Turkiya biyayya sau da kafa.