Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Turkiyya Ta Nemi a Mutunta Sakamakon Zabenta


Shugaban Turkiyya, Recep Tayyib Erdogan, ya fadi yau Litini cewa ya kamata duniya ta mutunta nasarar da jam'iyyarsu ta Adalci da ci gaba ta samu a zaben majalisar dokokin da aka gudanar, wanda ya bayyana da cewa zabin kwanciyar hankali mutanen kasar ta Turkiyya su ka yi.

Zaben na jiya Lahadi ya sake maida kasar ta Turkiyya kasa mai jam'iyyar siyasa guda, bayan watanni biyar kawai da jam'iyyar ta AKP ta rasa rinjayenta a majalisar dokokin kasar a karo na farko cikin sama da shekaru 10.

Jam'iyyar ta samu kashi 50% ne kawai wato kujeru 316 a Majalisar dokokin mai jimillar kujeru 550.

Babbar jam'iyyar adawa kuma CHP, ta sami dan sama da kashi kashi 25%, wanda ya tabbatar da wagegen gibin nasara ga jam'iyyar AKP fiye da yadda aka zata a baya.

Firaminista Ahmed Davutoglu ya bayyana aniyar hada kan kasa yayin da ya ke jawabi ga magoya baya a birnin Ankara da daren jiya Lahadi.

Ya kuma ce a samar da abin da ya kira sabuwar Turkiyya mai tsarin siyasar da ta dace.

Davutoglu ya sabunta kiraye-kirayen kwaskware kundin tsarin mulkin kasar, wani abu da jam'iyyar AKP ta nema don bai wa Erdogon karin ikon zartaswa.

Amma, duk kuwa da sabon rinjayenta a Majalisar dokoki, har yanzu jam'iyyar za ta kasa samun isassun kuri'u na yin gaban kai, wajen sabunta kundin tsarin mulki.

XS
SM
MD
LG