Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Sudan ta Kudu Da Madugun 'Yan Tawaye Zasu Tattauna A Ethiopia 20 Ga Wannan Watan


Firai Ministan Ethiopia Abiy Ahmed
Firai Ministan Ethiopia Abiy Ahmed

Ranar 20 ga wannan watan Yuni Shugaban Sudan ta Kudu Silva Kiir da madugun 'yan tawayen kasar Riek Machar zasu gana ido da ido a birnin Addis Ababa na kasar Ethiopia a wani yunkurin da Firai Ministan Ethiopian Abiy Ahmed ke yi na kawo karshen rikicinsu

Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir da jagoran ‘yan tawaye, Riek Machar, za su hadu gaba-da-gaba domin tattaunawa a ranar 20 ga watan Yuni a Addis Ababa, a wani yunkuri da Firai Ministan Ethiopia, Abiy Ahmed ke yi na shiga tsakani, domin a cimma matsaya ta zaman Lafiya tsakanin bangarorin biyu.

Kakakin Machar, ya fada a wata sanarwa da ya aike ta kafar email cewa, “sun yi na’ama da wannan yunkuri, kuma hakan zai kara kwarin gwiwa a kokarin da ake yi na neman maslaha.”

Nan take dai babu wani tsokaci da gwamnatin ta Sudan ta Kudu da kungiyar kasashen gabashin Afirka ta IGAD suka yi, dangane da wannan taro da aka shirya.

Amma, Kakakin Kiir, Ateny Wek Ateny, ya kwatanta goron gayyatar zuwa wannan taro a matsayin “mai muhimmanci.”

Kakakin jami’yyar SPLM mai mulki, Mabior Garang, ya tabbatarwa da shirin Muryar Amurka na “South Sudan in Focus” cewa, Machar zai taso daga Afirka ta Kudu zuwa Ethiopia domin halartar taron.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG