Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Sudan ta Kudu Na Neman Taimakon Ethiopia Ta Hana Amurka Gabatar da Kudurin Takunkumi a MDD


Shugaban Sudan ta Kudu Silva Kiir yayinda yake sauka a Addis Ababa babban birnin Ethiopia
Shugaban Sudan ta Kudu Silva Kiir yayinda yake sauka a Addis Ababa babban birnin Ethiopia

Silva Kiir na Sudan ta Kudu ya je Ethiopia, kwana daya kafin Amurka ta gabatar da kudurin kakabawa kasar takunkumi, yana neman taimakon Ethiopia ta hana Amurka cimma nasara a Majalisar Dinkin Duniya

Kwana daya kafin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya jefa kuri’ar akan shawarar da Amurka ta gabatar na azawa jami’an kasar Sudan ta kudu takunkunmin bisa zarginsu da sa kafar angulu ga shirin samun zaman lafiya a kasar, Shugaba Salva Kir na Sudan ta kudu ya bar birnin Juba zuwa birnin Addis Ababa na kasar Ethiopia. Zai bukaci taimakon kasar Ethiopia ta hana kaddamar da kudurin na Amurka.

Mai magana da yawun shugaban yace, shugaba Kir zai bukaci Prime Ministan Ethiopia yayi amfani da matsayin sa a zaman shugaban kungiyar habaka tattalin arzikin yankin da ake cewa IGAD a takaice, ya hau kujeran naki akan takunkunmin.

Kungiyar ta IGAD ta sha daukar dawainiyar yin shawarwarin samun zaman lafiya tsakanin bangarorin kasar Sudan ta kudu ta nufin farfado da yarjejeniyar samun zaman lafiya da aka kula a shekara ta dubu biyu da goma sha biyar ba tare da samun nasarar ba.

Kasar Ethiopia kuma, tana daga cikin kasashen da take da wakili na dindin din a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya. Yau Alhamis din nan ake sa ran wakilan kwamitin zasu jefa kuri’a akan kudurin na Amurka a birnin New York.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG