Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Raila Odinga Ya Ce Zai Iya Sasanta Shugaban Sudan ta Kudu Da 'Yan Tawaye


 Raila Odinga, tsohon Firai Ministan Kenya
Raila Odinga, tsohon Firai Ministan Kenya

Raila Odinga tsohon Firai Ministan Kenya kuma shugaban 'yan adawar kasar ya ce zai iya sasanta Shugaban Sudan ta Kudu Silva Kiir da jagoran 'yan tawyen kasar Riek Machar

Tsohon Firaministan Kenya Raila Odinga ya ce zai iya sasanta Shugaban Sudan Ta Kudu Salva Kiir da jagoran 'yan tawaye Riek Machar.

Odinga ya yi tayin jagorantar tattaaunawa tsakanin Shugagan kasar da tsohon Mataimakinsa don kawo karshen yakin basasar da aka kwashe shekaru kusan hudu da rabi ana gwabzawa a Sudan Ta Kudun.

Ya kai ziyara Juba cikin sirri don ganawa da Shugaba Kiir makwanni biyu da su ka gabata, 'yan kwanaki bayan da bangarorin da ke fafatawar su ka kasa cimma yarjajjeniyar zaman lafiya a Addis Ababa, babban kasar Habasha.

Ministan Yada Labaran Sudan Ta Kudu Michael Makuei ya fada yayin ziyarar cewa, Odinga ya bayyana cewa ya na so Kiir da Machar su sasanta kamar yadda shi da Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta su ka sasanta bayan bambance-bambancen suna baya.

Jaridar 'The EastAfrican'ta ruwaito cewa ana kyautata zaton Odinga zai tafi Afirka Ta Kudu a wannan makon don ya gana da Machar. Mai magana da yawun 'yan tawayen ya ce jami'an gwamnatin Afirka Ta Kudu sun yi daurin talala ma Machar bisa umurnin gwamnatin Kiir. To amma jami'an gwamnatin sun musanta zargin.


a

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG