Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

SUDAN ta KUDU:Har Yanzu Babu Yarjejeniyar Zaman Lafiya


Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir
Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir

Yayinda wakilan gwamnatin Sudan ta Kudu da wakilan 'yan tawaye ke ci gaba da tattaunawa har yanzu basu rabtaba hannu kan wata yarjejeniya ba duk da shawarwarin da Majalisar Dinki Duniya ta bayar da majalisar mijami'un kasar.

Har yanzu bangarorin da ke fafatawa da juna a Sudan ta Kudu, ba su rattaba hannu kan yarjajjeniyar zaman lafiya ba, bayan an shafe kwanaki biyar ana ta zafafan muhawara tsakanin wakilan a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, wanda ya sa masu shiga tsakanin na kungiyar Kasashen Kuryar Afirka (IGAD, a takaice) su ka tsara wani daftarin da ya tabo muhimman abubuwan da ake takaddama akai, da fatan bangarorin za su rattaba hannu akai zuwa karshen mako.

Wakilan gwamnatoci da ‘yan adawa da ‘yan raji da kuma masu saka ido sun rattaba hannu jiya Talata kan wata takarda ta alkawarin dukufa wajen cigaba da taunawa kan matsalolin shugabanci, ciki har da batun aiwatar da tanajin Majalisar Dinkin Duniya, MDD na bai wa mata akalla kashi 35% na matsayi a gwamnati ; da ajiye bindigogi, da kuma mutunta yarjajjeniyar tsagaita wutar da aka cimma a watan Disamban bara.

Shugabannin Majami’u suka jagoranci wannan zagaye na tattaunawar. Archbishop na Majami’ar Anglican na Sudan Ta Kudu Justine Badi ya fito daga wurin tattaunawar jiya Talata ya na mai cewa sakonsu ga wakilai a wurin tattaunawar mai sauki ne.

“Majalisar Majami’un Sudan Ta Kudu na kira ga bangarorin da su hada kai da juna, ta yin ba ni gishiri in ba ka manda; a kuma hada kai da kungiyar IGAD saboda a taimaka ma miliyoyin ‘yan Sudan Ta Kudu da ke fama,” abin da Badi ya gaya ma shirin Muryar Amurka mai suna Sudan in Focus kenan.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG