Hukumomi na dora alhakin faruwar wannan al’amari a wuyan wasu mutanen da suka kira masu safarar bil adama.
Mutane sama da 500 ne suka sauka a filin jirgin saman Diori Hamani a karshen mako a ayarin farko na almajiran da hukumomin Nijer suka kwaso daga kasar Senegal yayin da ayari na biyu ya zo da mutane a kalla 400, kafafen yadada labarai ne suka fara bankado labarin da ke nuna yadda wasu ‘yan Nijer suka mamaye titunan birnin Dakar da sunan bara akasarinsu mata da yara kanana mafari kenan da hukumomi suka dauri aniyar maido su gida.
Karancin abinci da talauci da matsalar tsaro ne kafafen na kasar Senegal suka bayyana a matsayin dalilan da suka sa wadanan ‘yan Nijer ficewa daga kasar don zuwa neman rayuwa mai inganci, abinda hukumomin Nijer suka karyata.
Gwamnan Yamai Oudou Ambouka na daga cikin mambobin tawagar jami’an gwamnati da suka tarbi wadanan almajirai. Ya kuma ce "cikin kashi goma, za ku samu 6 zuwa 7 na kananan yara. Abin tambaya shi ne, ta yaya wadannan yaran suka shiga wannan hali har su ka je Senegal? Yanzu tunda sun dawo, za a dau matakai na maida su har garinsu."
Ganin yadda wannan al’amari na bara ke bata sunan Nijer a idon duniya ya sa mahukunta suka dauri aniyar kwashe dukkan ‘yan kasar da ke waje da sunan wannan haramtacciyar sana’a wace alamu ke nuna cewa ba za a rasa hannun masu safarar bil adama ba a cikinta.
Kasashe irinsu Saudiyya da Aljeriya da Libya da Cote d’ivoire da jamhuriyar Benin na daga cikin wuraren da ‘yan Nijer suka saba tarewa da sunan bara, to amma bayanai na cewa tsauraran matakan da gwamnatocin wadannan kasashe suka dauka akan almajirai ya sa masu yin ta juya akala zuwa wajejen Senegal.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: