Wanna dai mataki ne da masu sharhi kan sha’anin tsaro ke ganin zai iya taimakawa a samu sassaucin matsalolin tsaro a yankunan iyakokin kasar da kasashe makwabta.
Zaman wanda ya gudana kwanaki kadan bayan da shugaban Nijar Janar Abdourahamane Tiani a wata hira da kafafen gwamnati ya zargi wasu kasashen yammacin Afrika da manyan kasashen yammacin duniya musamman Faransa da yunkurin haddasa hargitsi a kasar ta kasance wani lokaci na yiwa shugabannin al’umma wato sarakunan gargajiya bayani dangane da yanayin da kasa ke ciki a fannonin da suka hada da rayuwar al’ummar siyasa da sha’anin tsaro a cewar mai martaba sarkin Tsibirin Gobir Maradi Sultan Abdou Bala Marafa.
Sarakunan sun jaddada aniyar ci gaba da ba da gudunmawar da ta da ce don ganin an tunkari kalubalen tsaron da kasa ke fuskanta a halin yanzu.
A baya shugaban gwamnatin mulkin sojan Nijar Janar Abdourahamane Tiani dai ya gana da malamai magada annabawa domin ankarar da su cewa kasa na bukatar addu’oi a ci gaba da neman hanyoyin da za su taimaka a samu mafitar matsalolin da ake fuskanta a kasar.
Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:
Dandalin Mu Tattauna