Yayin da yake jawabi shugaban kwamitin kuma ministan ayyuka na musamman Barister Kabiru Tanimu Turaki ya yabawa jama'a da gwamnatin jihar bisa ga hadin kan da suke bayarwa lamarin da ya inganta zaman lafiya a jihar. Shugaban ya ce abun da muka gani ya bamu kwanciyar hankali. Mun ga jama'a da gwamnati da jami'an tsaro suna hada kai suna daukan matakai da suka inganta samun zaman lafiya da walwala tsakanin jama'a. Mutane sun fahimta cewa maganar tsaro bata jami'an tsaro ba ne kawai. Jama'a nada rawar da zasu taka.
Lokacin da gwamnan jihar ke karbar 'yan kwamitin ya bayyana irin halin da jama'arsa ke ciki. Ya ce kowa na rayuwa cikin kuntata domin hanyar cin abincin wasu an tauye masu.Masu saye da sayarwa kamar su masu toye-toye da sayar da tsire da makamanisu duk suna takure. Su kuma 'yan majalisar dokokin jihar kira suka yi ga jama'a da su ba dakarun tsaro hadin kai. Sun roki jama'a da su manta da abin da ya faru su nemi zaman lafiya saboda jihar ta koma yadda take da.
Yanzu dai jami'an tsaron iyaka su ne suke sintiri tsakanin iyakar Najeriya da Kamaru. Jami'an sun nemi hadin kai da jama'a domin a cigaba da samun zaman lafiya.
Ga Ibrahim Abdulaziz da karin bayani.