A wata sanarwa da rundunar ta ashirin da uku dake Yola babban birnin jihar ta ce dokar zata fara aiki ne yanzu daga karfe goma sha daya na dare zuwa karfe biyar na asubahi domin ba Musulman jihar damar yin azumi cikin walwala. Yayin da yake karin haske kakakin rundunar Kanal Ja'afaru Mohammed Nuhu ya ce al'umma su kiyaye doka domin zasu shiga wando kafa daya da duk wanda ya karya doka. Ya ce su zauna inda aka ce su zauna. Kada kuma su fita lokacin da bai dace ba.
Sassautawar ta zo daidai da lokacin da kwamitin dake neman sulhu da kungiyar Boko Haram wanda ke karkashin jagorancin ministan ayyuka na musamman Alhaji Tanimu Turaki ke kammala ziyarar da ya kai jihar ta Adamawa.Yayin ziyarar kwamitin ya gana da sarakuna da shugabannin addini a jihar inda shugaban kwamitin yake yabawa sarakuna bisa ga matakan da suke dauka na kirkiro sarakunan matasa lamarin dake taimakawa wajan kawo zaman lafiya.
A wani lamarin kuma wasu kananan hukumomi sun soma taimakawa al'umma da dokar ta baci tafi shafa musamman masu karamin karfi yayin da suke kokarin kama azumi. Shugaban karamar hukumar Jada cewa ya yi idan ba'a taimaka ma irin wadannan mutanen ba suna iya zama sanadiyar kara tabarbarewar tsaro.
Daga karshe gwamnan jihar Murtala Nyako ya yaba da addu'o'i da ake yi ya kuma ce a cigaba da yin addu'a musamman cikin watan azumi.
Ibrahim Abdulaziz nada rahoto.