Wata kungiyar yaki da cin hanci da rashawa, ta ayyana Amurka da Burtaniya, a matsayin kasashen da su ka fi aiwatar da dokokin hana kamfanonin cikin gida, bayar da cin hanci da rashawa a kasuwannin kasashen waje, kuma ta ce sauran manyan kasashe, kusan ba su ma yin komai.
Kungiyar ta Transparency Int’l, ta fadi yau dinnan Talata cewa kasar China, wadda ita ce kasar da ta fi fitar da kayan sayarwa a duniya, kusan ba ta yin komai don hana cin hanci da rashawa a huldar kamfanonin cikin kasar da sauran duniya.
Kungiyar, mai mazauni a birnin Berlin na kasar Jamus, ta ce kasashe hudu ne kadai daga cikin manyan kasashe 47 masu fitar da kayaki – wato Amurka, Burtaniya, Switzerland da kuma Isira’ila, wadanda kashi 16.5% na kayakin da ke kasuwannin duniya ne su ke samarwa – su ka aiwatar da dokokin hana kamfanomnin cikin gida bayar da cin hanci da rashawa a kasuwannin duniya zuwa shekarar 2019.
Wato kenan an samu raguwa daga kasashe 7 masu hakan, wadanda su ka samar da kayakin saidawa na kashi 27% a shekarar 2018.
Facebook Forum