Gabanin saukar shugaban, wanda tsohon mawakin kade-kaden Turawa ne, ya fadawa ‘yan Majalisar Haiti a birnin Port-Au-Prince cewa, zai sauka daga mulkin ne don ya bada tasa gudunmawar ga daidaiton kundin tsarin mulkkin kasarsu.
Inda ya mika ragamar mulkin kasar ga ita Majalisar da ke da tsananin tsaro, inda kuma ake jiran jin wanda ‘yan Majalisar za su zaba don ba shi rikon kwaryar mulki kafin lokacin da ya kamata a yi zaben shugaba na saosai.
Har ya zuwa yammacin Lahadin jiya din dai, ba wani kwakkwaran bayanin wanda zai gaji mulkin kasar mai fama da talauci don jan ragamarta na ‘yan wasu watanni zuwa lokacin zabe a kasar.