Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

New Hampshire: 'Yan Republican Za Su Yi Muhawara


2016 U.S. Republican Presidential Race
2016 U.S. Republican Presidential Race

Yayin da ya rage kasa da kwanaki uku a tunkari zaben fidda gwani a New Hampshire, ‘yan takarar neman shugabancin Amurka a karkashin Jam’iyyar Republican su bakwai za su sake wata muhawara a daren yau Asabar.

A wannan zabe ake sa ran wasu daga cikin ‘yan takarar za su yada makamansu idan masu zabe suka kada kuri’unsu.

A makon da ya gabata hamshakin mai kudin nan Donald Trump, ya ki haraltar wata muhawarar da aka shirya, saboda rashin jituwar da ya samu da kafar talbijin din da ta shirya muhawarar.

Jama’a a da dama dai sun soki wannan matakin kin halartar muhawarar da ya dauka, sai dai har yanzu babu wata alama da ta nuna cewa ko farin janinsa ya ragu a idon masu zabe.

Wannan muhawara har ila yau na zuwa ne a daidai lokacin da Trump din ke ci gaba da fama da alhinin kayin da ya sha a zaben Iowa, inda ya zo na biyu, bayan da Sanata Ted Cruz ya doke shi.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG