Shugaban kasar Ivory Coast Alassane Quattara yace zai tabbatar da ganin cewa, an kare hakkokin bil’adama a kasarshi. A cikin hirar da Muryar Amurka tayi dashi jiya jumma’a, Mr. Quattara ya bayyana cewa, zai kafawa duk wani dan kasar Ivory Coast da ya keta hakin bil’adama takunkumi. Ya kuma musanta cewa, har yanzu tsofaffin kungiyoyin ‘yan tawaye ne ke iko da galibin kasar. Bisa ga cewarshi, shi mutum ne mai kaunar zaman lafiya, kuma shine shugaban dukan mutanen kasar Ivory Coast. Kungiyar kare bakin bil’adama Amnesty International ta bada rahoto makon nan cewa, dubun dubatan yan gudun hijiran kasar Ivory Coast suna fargaban komawa gidajensu sabili da gudun kada dakarun dake goyon bayan shugaba Quattara su kai masu hari. Mr. Quattara ya yi hira da tashar Muryar Amurka ne a Washington jim kadan bayan shi da wadansu shugabannin kasashen yammacin Afrika uku suka gana da shugaban Amurka Barack Obama. Mr. Quattara ya bayyana nasarar zaman. Bisa ga cewarshi, shugaba Obama ya bayyana gamsuwa da aikin da shugabannin ke yi , yayinda shugabannin na Afrika kuma suka nemi tallafin domin bunkasa kasashensu. Sauran shugabannin kasashen nahiyar Afrikan uku da suka gana da shugaba Obama sun hada da shugaban kasar Benin Boni yayi, da na Niger Mahamadou Issoufou da kuma na kasar Guinea Alpha Conde. A cikin jawabinsa, shugaba Obama yace dukan shugabannin hudu suna iya zama abin koyi a nahiyar, da cewa, dukansu sun hau karagar mulki ne bayan gudanar da zabe mai sahihanci, kuma sun nuna naciya duk da kalubalai da suke fuskanta. Bisa ga cewarshi, kalulabar da kasar Ivory Coast ke fuskanta ta hada da tilastawa tsohon shugaban kasar Laurent Gbagbo mutunta sakamakon zaben da kasashen duniya suka amince da shi.
Shugaban kasar Ivory Coast Alassane Quattara yace zai tabbatar da ganin cewa, an kare hakkokin bil’adama a kasarshi.