Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sanda Sun Yi Arangama Da Masu Zanga-Zanga A Kasar Guinea


Magoya bayan hamayya na Guinea dauke da kwalin da aka rubuta "Zaben Gaskiya - Alamar Zaman Lafiya" lokacin wani gangamin da 'yan hamayya suka yi a Conkary ranar 31 Maris 2012, su na neman da a yi zaben 'yan majalisar dokoki na gaskiya a kasar.
Magoya bayan hamayya na Guinea dauke da kwalin da aka rubuta "Zaben Gaskiya - Alamar Zaman Lafiya" lokacin wani gangamin da 'yan hamayya suka yi a Conkary ranar 31 Maris 2012, su na neman da a yi zaben 'yan majalisar dokoki na gaskiya a kasar.

An ce mutane akalla 15 sun ji rauni lokacin da aka yi artabu a tsakanin masu zanga-zanga da 'yan sanda da kuma magoya bayan shugaban kasar

‘Yan sanda a kasar Guinea sun yi amfani da barkonon tsohuwa da kulakai domin tarwatsa ‘yan zanga-zangar dake neman gwamnati ta fara tattaunawa da ‘yan hamayya game da gudanar da zaben ‘yan majalisar dokokin da aka jima ana jinkirtawa.

Wani wakilin Muryar Amurka a Conakry, babban birnin kasar, yace an bai wa hammata iska a tsakanin ‘yan zanga-zangar, da ‘yan sanda da kuma wasu matasa masu goyon bayan shugaba Alpha Conde.

Wani madugun ‘yan hamayya, Cellou Dallein Diallo, yayi jawabi ga masu zanga-zangar, yana mai fadin cewa, "masu zanga-zangar su na nema ne da a mutunta hakkinsu, kuma zasu sake bazuwa kan tituna a (yau) jumma’a, da kuma a kwanakin dake tafe har sai sun samu nasara."

An ba da rahoton cewa mutane akalla 15 sun ji rauni a wannan arangama.

An shirya gudanar da zaben a ranar 8 ga watan Yuli, amma a watan da ya shige shugaba Conde ya fito ya dage yana mai cewa akwai matsala game da tsarin rajistar sunayen masu jefa kuri’a. ‘Yan zanga-zangar su na kiran da a yi garambawul ga hukumar zabe, a kuma sake nazari tare da binciken kundin rajistar masu jefa kuri’a.

An gudanar da zaben ‘yan majalisar dokoki na karshe a kasar Guinea a shekarar 2002, a zamanin shugaba Lansana Conte.

Kungiyar Tarayyar turai, wadda ta tsinke bayar da agaji ga kasar Guinea a bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a 2008, ta ce ba zata maido da shirye-shiryen bayar da tallafi ba har sai an gudanar da wannan zabe.

XS
SM
MD
LG