Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matasan Yankin Sahel Sun Fara Neman Mafita Akan Matsalolin Da Suke Fuskanta


Matasa da ga yankin Sahel a lokacin wani taro na musamman a birnin Agadez din Jamhuriyar Nijar.
Matasa da ga yankin Sahel a lokacin wani taro na musamman a birnin Agadez din Jamhuriyar Nijar.

Matasan yankin Sahel sun gudanar da taro da nufin tattauna a kan manyan kalubalen da suke cin karo dasu a wannan yanayi da kasashen uku dake yankin Sahel ke fama da matsalolin da suka dabaibaye su.

Matasa fiyeda 200 ne suka fito daga jihohi takwas na Nijar, hade da matasan kasashen Mali da Burkina Faso suka kammala wani taro a birnin Agadez dake arewacin Jamhuriyar Nijar inda suka tattauna a kan matsalolin da ke addabarsu domin samun mafita.

Matasan sun kuma tattauna kan hanyoyin samun mafita kan wadannan kalubale dake gabansu wadanda ke kawo musu cikas ga cigaban rayuwarsu.

Birnin Agadas ne ya karbi bakunci taron matasan inda suka shafe kwanaki biyar suna sada zumunci da samar da hadin kai a tsakaninsu.

Mahamadu Umaru, wanda matashi ne da ya fito daga jihar Maradi, yace wajibi ne matasan Afirka su tashi tsaye domin samarwa kansu ingantacciyar rayuwa.

Shi kuma Sidi Mohamed wanda shine Shugaban Majalisar Matasan Kasar Nijar, kira yayi ga matasan da su hada kansu domin samar da cigaba ga kasashensu.

Daga karshen taron, matasan sun fitar da wani kundi wanda a cikinsa akwai shawarwarin da zasu gabatar ma hukumomin kasashen wanda suke ganin idan anyi anfani dasu za’a iya magance matsalolin da matasan ke cin karo dasu a kasashen dake yankin Sahel.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG