AGADEZ, NIGER - An shafe kusan minti takwas ana fafatawa tsakanin ‘yan kokowar kafin Kadiri Abdou ya samu nasara akan Mati Souley.
Wannan ne karo na shidda da dan kokawar na Dosso ke nasarar lashe takobi na Nijar, inda ya kafa tarihin da babu wani daga cikin ‘yan wasan kokawa da ya taba kafa shi.
Firai Ministan Nijar Ali Lamine Zaine tare da tawagarsa, da Firai Ministocin kasashen Mali da Burkino Faso ne suka jagoranci bikin rufe gasar kokawar gargajiyar karo na 44, inda ya yaba da yadda aka gudanar da wasannin.
‘Yan Nijar dai na fatan ganin sauya fasalin yadda ake gudanar da wasannin kokawar sakamakon yadda ake samun matsalolin a yayin fafatawar.
Kamar kowace shekara, ‘yan Nijeriya da dama ne suka halarci kwanbalar ta kokawar gargajiya a bana inda suma suka yaba da yadda aka yi wasannin.
Kwanaki goma aka shafe ana fafatawa tsakanin ‘yan wasan kokawar gargajiya na Nijar guda 80 da suka fito daga jihohi takwas na kasar.
A shekara ta 1975 ne aka soma kokawar gargajiya domin sada zumunta tsakanin dukkan jihohin Nijar.
To saidai a tarihin kokawar gargajiya a Nijar ba’a taba samun wanda ya yi bajinta kamar Kadiri Abdou ba na jihar Dosso ba.
Saurari cikakken rahoto daga Hamid Mahmoud:
Dandalin Mu Tattauna